Shugaban Kasa Buhari yayi watsi da kowa bayan hawan sa mulki – Ghali Na’abba

Shugaban Kasa Buhari yayi watsi da kowa bayan hawan sa mulki – Ghali Na’abba

Mun ji cewa Rt. Hon. Ghali Umar Na’abba wanda Tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Tarayya na kasar nan ne a lokacin Shugaban Kasa Obasanjo yace akwai matsala a tafiyar Jam’iyyar APC mai mulki.

Shugaban Kasa Buhari yayi watsi da kowa bayan hawan sa mulki – Ghali Na’abba
Ghali Na’abba yace Shugaban Kasa Buhari ne silar rikicin APC

Ghali Na’abba wanda ya bar PDP a 2015 ya sauya sheka zuwa APC yace yayi da-na-sanin dawowa Jam’iyyar ta APC mai mulki. Na’abba yace Shugaba Buhari ne ke kadai ke yin yadda ya so a Jam’iyyar kuma babu wanda ya isa yayi magana.

Tsohon Shugaban Majalisar Kasar yace sam babu hadin kai a Jam’iyyar APC. Na’abba ya cigaba da cewa ba ayi da shi ne a APC saboda kurum yace ba ya tare da tazarcen Shugaban Kasa Buhari. Na'abba yace yanzu an daina kiran sa wajen taron APC.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta rasa wani kujera a Jihar da ta ke mulki

Na’abba yace Shugaba Buhari ba ya aiki da Jam’iyyar da ta kawo sa mulki, tsohon ‘Dan Majalisar yace babu wanda Buhari yake aiki tare da shi illa iyaka kurum yayi abin da ya ga dama don haka ne ma wadanda ke tare da shi su ka rabu da shi.

Tsohon Kakakin Majalisar kasar a lokacin PDP yace a dalilin Shugaba Buhari ne aka rika samun matsaloli wajen zaben Shugabannin Jam’iyyar APC a Jihohi da dama. Na’abba yace bayan an ci zabe Buhari yayi watsi da kowa sai ‘Yan ACN da CPC.

Kamar yadda Na’abba ya bayyana, Shugaban Kasar ba ya aiki da Majalisa ba kuma ya aiki da Jam’iyyar APC. Don haka ne ma wadanda ke ganin ba ayi da su ke barazanar ficewa daga Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel