Duk karya ce da damfara: Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso a kan fitar da dalibai karatu kasashen waje

Duk karya ce da damfara: Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso a kan fitar da dalibai karatu kasashen waje

- Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso a kan fitar da dalibai karatu kasashen ketare, y ace duk karya ce da damfara

- Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya caccaki tsohon gwamna, Rabi’u Musa Kwankwaso a kan tsarin tallafawa dalibai

- Ganduje ya bayyana shirin a matsayin damfara saboda daliban da aka fitar sun samu dammar kwakular kudaden gwamnati ne kawai

Ganduje ya dauki alkawarin gyara tare da tsaftace tsarin fitar da dalibai karatu kasashen ketare da zarar an sake zaben sa a karo na biyu

Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar ganduje, ya yi kaca-kaca da tsarin tsohon gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso na fitar da dalibai karatu zuwa kasashen ketare tare da bayyana cewar shirin hanya ce kawai ta damfarar gwamnati.

Duk karya ce da damfara: Ganduje ya yi kaca-kaca da Kwankwaso a kan fitar da dalibai karatu kasashen waje
Ganduje da Kwankwaso

Jaridar Daily sun ta rawaito cewar Ganduje ya fadi hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai tare da daukan alkawarin gyara tare da tsaftace shirin bayar da tallafin karatu ga dalibai zuwa kasashen ketare da zarar an sake zaben sa karo na biyu.

Kazalika, Ganduje ya musanta kalaman Kwankwaso na cewar ya biya dukkan kudin karatun daliban da ya fitar zuwa kasashen tare, ya kara da cewar gaskiyar Magana it ace; gwamnatin sat a biya kudin kafin alkalami ne kawai na daliban amma ba dukkan kudin karatun su ba.

DUBA WANNAN: Sanata Hunkuyi ya yi kaca-kaca da El-Rufa'i, ya kira shi da takadari

Gwamna ya jajanta yadda aka dinga amfani da dillalai wajen fitar da daliban, dalilin da ya sa kudin da aka kashe a kan daliban jihar Kano ya zarce yadda jami’o’in ke cajin ragowar dalibai.

A bangaren nagartar abinda daliban suka karanta a jami’o’in da suka fita, Ganduje, y ace wasu jami’o’in sun fara koyar da darussa da aka tura daliban jihar Kano su karanta ne kawai bayan karbar makudan kudi daga gwamnatin Kano, amma a zahiri basa koyar da darussan a baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng