An gano wani direban jirgin saman Rasha a Afghanistan bayan shekaru 30 da bacewa
- An gano wani matukin jirgin saman Rasha a kasar Afganistan bayan shekaru 30 da bacewarsa
- Matukin jirgin ya bace ne tun bayan abokan gaba sun harbo jirginsa a shekarar 1987 da tarayyar Soviet ke yaki a kasar Afganistan
- An ruwaito cewa matukin jirgin ya bayyana cewa yana son ya dawo gida
An gano wani matukin jirgin sama dan kasar Rasha wanda akayi tsamanin ya mutu bayan an harbo jirginsa a shekarar 1987 lokacin da tarayyar Soviet suka kai taimako a kasar Afganistan kuma ya nuna niyyar sa ta dawowa gida kamar yadda wata kungiyar tsaffin soji na Rasha suka bayyana a wata rahoton jaridar Guardian.
Shugaban kungiyar sojin kasar Rasha masu saukan ungulu, Valery Vostrotin, ya shaidawa kafar yadda labarai na RIA Novosti a ranar Juma'a 1 ga watan Yuni cewa, "Yana nan da ransa. Abin al'ajabi ne. Sai dai yanzu yana bukatar taimako."
KU KARANTA: Gangancin tuki ya yi sanadiyyar rasuwar mutane 6 da raunata wasu 11
Vostrotin wanda shi ke sanya idanu kan sojojin hadin gwiwar kasar Rasha da Amurka wanda suka mutu a filin daga ko kuma aka kama su a matsayin fursunonin yaki ya nemi a sakayya sunan matukin jirgin saboda tsaro.
Mataimakin kungiyar tsaffin sojoji mai suna Battle Brotherhood, Vyacheslav Kalinin, ya shaidawa manema labarai cewa an harbo matukin jirgin ne wanda a kalla ya wuce shekaru 60 a shekarar 1987. Kalinin ya yi ikirarin cewa watakila matukin jirgin yana kasar Pakistan inda kasar Afganistan ke ajiye fursunonin yaki kuma ya ce yana son ya dawo gida.
Jaridar Kommersant business daily ta ruwaito wani labari mai kama da wannan inda ta ce matukin jirgin tarayyar Soviet guda daya ne katchal mai suna Sergei Pantelyuk ya bace a yakin na shekarar 1987 bayan an harbo jirginsa da ta taso daga Bagram Airfield wanda a yanzu ya zama sansanin sojin Amurka a arewacin Kabul.
Shugaban kungiyar tsaffin sojojin da suka hallarci yaki ya ce mahaifiyar Pantelyuk da kanwarsa suna da rai kuma wata jaridar Komsomolskaya Pravda ta binciko inda diyar sa mai shekaru 31 ta ke.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng