Hukumar NDLEA ta cafke Miyagu 85 da Kilo 668 na Muggan 'Kwayoyi a Jihar Zamfara
Hukumar hana fatauci da muggan kwayoyi ta Kasa, NDLEA (National Drug Law and Enforcement Agency) ta cafke miyagu 85 masu dillanci da safara muggan kwayoyi tare da samun nasarar damke kilo 668.6 na muggan kwayoyi a tsakanin watan Janairu zuwa Yunin 2018.
A ranar Juma'ar da ta gabata ne Kwamandan reshen Jihar Zamfara, Mista Gabriel Eigege, ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a babban birnin Jihar na Gusau.
Eigege yake cewa, hukumar ta samu nasarar damke miyagun mutane 85 masu dillanci da fataucin muggan kwayoyi cikin watanni biyar da suka hadar da Mata 4 da kuma Maza 81.
A yayin da hukumar ke ci gaba da gudanar da bincike domin tsarkake jihar Zamfara daga muggan kwayoyi, ta kuma samu nasarar cafke wasu 'yan ta'adda 10 cikin Birnin Gusau tare da mallakin muggan makamai a ranar 20 ga watan Janairun 2018.
Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar ta mika wannan 'yan ta'adda zuwa ga hukumomin da suka dace domin ci gaba da bincike a kansu.
Mista Eigege ya ci gaba da cewa, hukumar za ta gurfanar da wannan miyagu a gaban Kuliya da zarar ta kammala binciken ta domin zartar masu da hukunci da suka dace daidai da laifukan da suka aikata.
KARANTA KUMA: PDP ta barrantar da kanta daga ikirarin Orji Kalu na Kashe Abokan Adawa
Rahotanni da sanadin kamfanin dillancin labarai na Najeriya sun bayyana cewa, a ranar 23 ga watan Mayun da ta gabata hukumar ta NDLEA ta cafke wasu miyagu biyu dauke da muggan kwayoyi har sama da kilo 500 na maganin Codeine da Rafanol a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
A ranar 30 ga watan Mayun da ya gabata ne hukumar ta kuma cafke wasu mutane uku a babbar hanyar Gada Zaima dauke da wasu makamai da ake zargin bama-bamai ne.
Kwamandan ya kuma nemi al'ummar jihar akan su ci gaba da tallafawa hukumar da rahotanni da za su taimaka wajen dakile ta'ammali da fataucin muggan kwayoyi a jihar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng