MTN zata biya tara saboda kwashe kudi don saya wa kwastomomi data ba izini

MTN zata biya tara saboda kwashe kudi don saya wa kwastomomi data ba izini

- Kamfanin MTN ya saba sace wa kwastomominsa kudi daga waya bisa karya

- A yanzu dai NCC ta sanyo su gaba saboda satar tayi yawa

- Matsalar itace, ana kwashe kudi ace ka sayi data bayan baka yi niyya ba

MTN zata biya tara saboda kwashe kudi don saya wa kwastomomi data ba izini
MTN zata biya tara saboda kwashe kudi don saya wa kwastomomi data ba izini

Kamfanin MTN zai biya tarar N5,000,000 ga gwamnatin Najeriya ta hannun NCC muddin aka same shi da laifin sake sace wa kwastomomi bayan sun sanya kati a wayoyinsu na salula. Satar tana zuwa ne ta hanyar sayen data ko waka ko wasu shirmen dai da mutum ya taba yi a baya, amma ba da niyyar sake saya ba.

A yanzu NCC tace kada a sake saya wa masu amfani da wayar salula abubuwan da basu yi oda ba kuma basu siya ba. Tarar zata shafi MTN ne amma ana sa rai nan gaba zata shafi sauran layuka.

Hukumar sadarwa ta Najeriya(NCC) ta umarci kamfanonin sadarwar kasar, dasu guji sabuntawa kwastomomi data packages ba tare da izini ba. In kuwa aka kamasu da laifin, za a ci su tarar Naira miliyan 5.

NCC tace jan kunnen ya zama dole ne sakamakon korafe korafen da masu amfani da layikan keyi na kamfanonin.

A ranar 21 ga watan Mayu, 2018 ne NCC ta bada umarni ga duk kamfanonin sadarwan dasu guji sabuntawa kwastomomi data packages ba tare da yardar su ba.

Zababben mataimakin shugaban NCC ya karanto zanga zangar tataunawa da kwastomomi suka a ranar Alhamis, a karu, jihar Nasarawa.

Zababben mataimakin shugaban, wanda daraktan arewa ta NCC, Mrs Helen Obi ta wakilta tayi bayanin korafe korafen da suke samu yasa bazasu jinkirta sanar da ma'aikatan umarnin ba.

DUBA WANNAN: Ashe an jima Yarima Salman ciwo ne yayin kokarin juyin mulki

Bayan tarar Naira miliyan 5 da zata biyo bayan karya dokar, ya kara bayyanawa cewa duk rana daya da aka yanke hukuncin ba a biya tarar ba, zai janyo karuwar Naira 500,000.

"Yakamata kamfanonin sadarwan su tura sakon karta kwana ga masu amfani da layikan kafin sabunta, sannan su kara maimaita tura sakon don tabbatar da cewa an fahimci abinda sakon ya kunsa. A duk lokacin da masu amfani da layikan suka kawo karar kamfanin sadarwan sakamakon karya dokar, kamashon zai daukaka korafin.

Yanzu kam wannan na nufin kwastomomi zasu daina rasa kudinsu ta hanyar zamba da ake yi musu a layukansu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng