An Zartar da Hukuncin Kisa kan Wata Saniya 'dauke da Juna Biyu bisa laifin 'Ketare Iyaka

An Zartar da Hukuncin Kisa kan Wata Saniya 'dauke da Juna Biyu bisa laifin 'Ketare Iyaka

Da sanadin shafin Jaridar The Punch, mun samu rahoton cewa an zartar da Hukuncin Kisa kan wata Saniya mai dauke Juna Biyu sakamakon laifin da ta aikata na ketare iyaka.

Rahotanni sun bayyana cewa babban laifin da wannan Saniya mai Juna Biyu ta aikta shine tayi tattaki daga gonar da take kiwo dake cikin kungiyar Kasashen Turai a Kasar Bulgaria zuwa Kasar Serbia da ba ta cikin jerin kungiyar Kasashen na Turai.

Ana sa ran Wannan jar Saniya mai sunan Penka za ta haife abin da ke cikin ta nan da watanni uku maso gabatowa kamar yadda rahotanni da sanadin Jaridar Daily Mail ta ruwaito.

Tsautsayi gami da karar kwana dake afkuwa ba tare da wata sanarwa ba ya sanya wannan Saniya mai sunan Penka ta bar cikin garken 'yan uwanta na Shanu dake Kauyen Kopolovtsi inda ta tsallake iyaka zuwa cikin kasar Serbia.

An Zartar da Hukuncin Kisa kan Wata Saniya 'dauke da Juna Biyu bisa laifin 'Ketare Iyaka
An Zartar da Hukuncin Kisa kan Wata Saniya 'dauke da Juna Biyu bisa laifin 'Ketare Iyaka

Bayan makonni biyu da tafiya gantali da wannan Saniya ta yi, wani Manomi ya dawowa da mai ita, Ivan Haralampiev a gabar iyakar Kasashen biyu ba tare da ketarewa ba.

A sanadiyar haka ne hukumomin kasar Bulgaria su ka bayyana cewa dole sai an kawar da wannan Saniya daga doron Kasa sakamakon tsauraran dokoki da kungiyar Kasashen Turai ta shimfida.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Sama ta dauki Sabbin Dakaru 7, 000 cikin shekaru 3

A halin yanzu dai an zartar da hukuncin kisa kan wannan Saniya da ba ta ji ba kuma ba ta gani ba sakamakon rashin takardu da suka dace duk da Likitocin Dabbobi na kasar Serbia sun tabbatar da ingatacciyar Lafiyar ta.

Mamallakin wannan Saniya, Ivan Haralampiev yayi koken a tseratar da jinin Dabbar sa yayin ganawa da gidan talabijin na BNT a ranar Alhamis din da ta gabata.

Hukumomin Kasar Bulgaria sun bayyana cewa ba su da ikon tseratar da rayuwar Penka a sanadiyar dokokin da suke tattare da Kungiyar kasashen Turai, inda suka nemi a kawar da ita daga doron Kasa ba tare da wani tsaiko ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel