Buhari ya sha ruwan yabo a wajen Ekwaremadu saboda sanya hannu da yayi a dokar ba matasa damar takara

Buhari ya sha ruwan yabo a wajen Ekwaremadu saboda sanya hannu da yayi a dokar ba matasa damar takara

Mataimakin shugaban majalisar dattawa Ike Ekweremadu, ya yabama shugaban kasa Muhammadu Buhari akan sanya hannu da yayi a dokar rage shekarun tsayawa takara wato “Not-Too-Young-To-Run’’.

An kafa dokar ne domin kundin tsarin mulki ta bayar da damar da za’a rage shekarun masu takara na wasu mukaman siyasa.

Ya kuma bayyana cewa majalisar dokokin kasar ta cika alkawarinta.

Buhari ya sha ruwan yabo a wajen Ekwaremadu saboda sanya hannu da yayi a dokar ba matasa damar takara
Buhari ya sha ruwan yabo a wajen Ekwaremadu saboda sanya hannu da yayi a dokar ba matasa damar takara
Asali: UGC

Ekwremadu wanda ya kuma kasance shugaban kwamitin duba na kundin tsarin mulkin 1999, yace wannan sabon gyara da akayi ga kundin tsarin mulki zai ba matasan Najeriya damar da za’a dama da su a harkar siyasa.

KU KARANTA KUMA: Jirgin sama yayi saukan bazata sakamakon warin jikin wani fasinja da ya sa sauran mutane amai da suma

Ya kuma bukaci shugaba Buhari da ya sanya hannu a sauran gyare-gyare na kundin tsarin mulki dake jiransa inda ya bayyana su a matsayin masu tsanani ga shugabanci nagari a kasa.

A halin da ake ciki, jam'iyyar PDP tace ita ce sanadiyan tabbatar da wannan doka na ba matasa damar shiga siyasa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng