Yana zargin matarsa da yin ashararanci da juya masa baya a shimfida
Wani magidanci mai suna Hammed Akinleye ya roki kotun Customary da ke Iyana-Ofa, Ibadan a jihar Oyo ta rabar aure tsakaninsa da mai dakinsa Mrs. Olabisi Akinleye.
Ya yi ikirarin cewa matarsa tana kaurace masa a shimfidarsu ta aure amma ta kuma tana bayar da kanta ga wasu mazaje a waje.
Olabisi wadda ma'aikaciyar jinya ce ta shigar da kara kotun tana neman a raba aurensu na shekaru bakwai bayan da shaidawa kotu cewa ya kulle mahaifiyarta a caji ofis.
KU KARANTA: Asiri ya sake tonuwa: Wata daliba ta sake tona asirin wani Farfesa da ke neman kwanciya da ita
Ta kuma ce mijin baya kyautata mata bayan tun da farko dabara ya yi mata ta aureshi.
Har ila yau, ta ce Hammed ya yi wa Yan sanda karya inda ya fada musu cewa ta sace masa kudi kuma ta boye a gidan mahaifiyarta.
Kalamanta, "Miji na bashi da gaskiya ko kadan, ya yi min karya cewa ya auri wata mata a baya kuma ta rasu sakamakon hatsarin mota.
"Ya zo a siffan bazawari kuma ya roke ni in aure shi. Sai dai bayan ya yi min ciki, sai ya bukaci in zubar da cikin yana mai cewa ba zai iya aure na ba saboda na haihu tare da wani mutum ba tare da aure ba."
Sai dai Hammed ya musanta dukkan maganganun da ta fadi a kansa, ya kuma kara da cewa ya gaji da halinta na bin wasu mazaje a waje.
"Ina son kotu ta amsa bukatar mata na na raba auren mu, nayi farin ciki da ta taso da batun. Ba zan iya jure irin cin amanar da ta ke min ba. Ba ta bani hakki na na kwanciyar aure. Dulk lokacin da na kusance ta sai ta ce bata da lafiya alhalin tana bin wasu mazaje ne," inji shi.
Shugaban kotun, Mr. Mathew Ogungbenle ya dag sauraron karar har zuwa ranar 6 ga watan Yunin 2018, ya kuma umurci ma'auratan su zo tare da iyayensu a ranar da za'a cigaba da saurarn shari'ar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng