Kaico! Mayakan Boko Haram sun kashe Sojoji 5 a harin kwantan ɓauna
Akalla dakarun rundunar Sojan Najeriya ne suka gamu da ajalinsu a wata harin kwantan bauna da mayakan kungiyar ta’addanci ta Boko Haram ta kai ma tawagar Sojojin Najeriya a jihar Borno, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 31 ga watan Mayu, a karamar hukumar Gwoza na jihar Borno, kamar yadda Kaakakin rundunar Sojin kasa, Birgediya Texas Chukwu ya tabbatar.
KU KARANTA: Hattara mata: Daga haduwa a Facebook wata budurwa ta rasa budurcinta a hannun wani Kato
Sanarwar ta bayyana cewa bataliya ta 271 na rundunar Sojojin Najeriya dake gudanar da aikin yaki da yan ta’adda a yankin Arewa maso gabas sun fada wata tarko da yan ta’adda suka shirya a daidai kauyen Pridang-Bitt.
“Sojojin sun fada kan wasu bamabamai da yan ta’adda suka binne, daga bisani yan ta’addan suka yi musu kawanya, a nan aka fara musayar wuta, inda aka yi kare jinni biri jini, Yan ta’adda da yawa sun mutu, amma Sojoji biyar sun rasa rayuwansu.” Inji Texas.
Sanarwar ta karkare da cewa tuni aka kwashe gawarwakin Sojojin da suka rigami gidna gaskiya, inda aka garzaya dasu zuwa babban asibitin Sojoji dake garin Maiduguri.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng