2019: Zan azurta ku da miliyoyi idan ku ka sake zabe na - Gwamnan wata jihar Arewa

2019: Zan azurta ku da miliyoyi idan ku ka sake zabe na - Gwamnan wata jihar Arewa

A jiya Talata 30 ga watan Mayu ne gwamnan jihar Taraba, Darius Dickson Ishaku, ya nemi hadin kan matasan jihar don jefa masa kuri'a a takarar da zai sake yi karo ni biyu tare da yi musu alkawarin cewa za su mallaki miliyoyin naira.

Gwamnan ya yi wannan jawabin ne a bukin cika shekararsa uku a mulki wanda ya yi dai-dai da bukin zagayowar ranar demokradiya ta Najeriya da akayi a filin motsa jiki na Jalingo.

2019: Zan azurta ku idan ku ka sake zabe na - Gwamnan wata jihar Arewa
2019: Zan azurta ku idan ku ka sake zabe na - Gwamnan wata jihar Arewa

"Ina bukatar ku (matasa) ku fito ku zabe mu idan lokacin zabe ya zo. Zan tallafa muku ku mallaki miliyoyi: za ku rika fitar da madara da nama kuna sayar wa a kasashen waje; za ku rika tuka mota kirar Marsandi a maimakon a dai-daita sahu," inji shi.

KU KARANTA: An shiga alhini a Ikorodu bayan wutar lantarki ta kashe ma'ikaci a lokacin da ya ke gyara

Gwamnan ya ce a shekarar 2015 lokacin da ya dare kan kujeran mulki, akwai dimbin matasa da basu da ayyukan yi da ke zaman kashe wando.

"Amma a yau, sama da matasa 3000 sun sami ayyukan yi kuma an karfafa wasu dubai ta hanyar koyar da su sana'a a karkashin shirin Rescue Mission da gwamnatin sa ta kirkiro.

"Wadanda aka koyar da su sana'a sun tsaya da kafarsu har ma suna daukan wasu aiki. Labarin wata matashiya Aisha misali ne mai kyau; An koyar ta ita sana'a daga baya kuma ta dauki wasu mutane shida aiki a karkashinta."

Gwamna Ishaku ya ce gwamnatinsa ta taka rawar gani a shekaru ukun da tayi a mulki kuma ya tabbatarwa mutane Taraba cewa zai cika dukkan alkawurran da ya dauki yayin yakin neman zabe a sauran shekar daya da ya rage masa.

Mataimakin gwamnan, Haruna Manu ya ce gwamnatin gwamna Ishaku ta cika dukkan alkawurran da ta dauka wa al'umma a karkashin shirin Rescue Agenda kuma ya mika godiyarsa da mutane Taraba tare da neman kuri'unsu a zabe mai zuwa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164