An shiga alhini a Ikorodu bayan wutar lantarki ta kashe ma'ikaci a lokacin da ya ke gyara

An shiga alhini a Ikorodu bayan wutar lantarki ta kashe ma'ikaci a lokacin da ya ke gyara

- Wani ma'aikacin kamfanin lantarki da ke Ikeja ya rasu yayin da ya ke kokarin gyaran wutar lantarki

- Wani ma'aikacin kamfanin ne ya kunna wutan cikin kuskure ba tare da ya san marigayin na kan pole waya ba

- Duk kokarin da akayi ne ceto rayuwarsa bai yi tasiri ba saboda a nan take ya rasu

Wani ma'aikacin kamfanin rabar da wutan lantarki na Ikeja Electricity Distribution Company (IKEDC) ya rasu a jiya Laraba 30 ga watan Mayu yayin da yake kokarin gyara wutar lantarki da masu aikin titi suka lalata.

Abin tausayi ya faru ne a Olainukan Bus Stop, Isawo, Ikorodu kuma a nan take ma'aikacin kamfanin wutan lantarkin ya rasu sakamakon ilar da wutar tayi masa kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

An shiga alhini a Ikorodu bayan wutar lantarki ta kashe ma'ikaci
An shiga alhini a Ikorodu bayan wutar lantarki ta kashe ma'ikaci

Legit.ng ta gano cewa an matsar da sandunan wutan lantarkin ne saboda gyaran titin da akeyi sakamakon hakan kuma wutan lantarki ya samu matsala a yankin.

KU KARANTA: Kasar Saliyo ne bidar likitoci da malaman makaranata daga Najeriya

Kamfanin ta aike da wasu daga cikin ma'aikatan ta suyi gyara a wajen bayan wasu daga cikin mazauna unguwar sun shigar da kara.

Da isar su wajen, daya daga cikin ma'aikatan ya dare sandan wutar domin ya yi gyaran yayinda sauran abokan aikinsa suka tsaya a kasa domin taimaka masa.

Sai dai kwatsam abubuwa sun rikice bayan wani daga cikin ma'aikatan da ke ofishin hukumar samar da lantarkin ya kuna wutar a yayin da marigayin ke sama yana gyara wanda hakan yasa wutar tayi masa lahani.

Abokan aikinsa sunyi iyaka kokarinsu don ganin sun ceto rayursa sai dai babu wani abu da suka za su iya yi don taimakonsa.

Rasuwar ma'aikacin lantarkin ya jefa dukkan unguwan cikin juyayi da dimuwa.

A wata rahotan, Legit.ng ta ruwaito muku yadda wani ma'aikacin wutan lantarki, Usaini Usman ya rasu a Kano sakamakon ilar da wutar tayi masa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164