Na yafewa Kwankwaso da mabiyansa yan Kwankwasiyya - Ganduje
Rahotanni dake zuwa mana sun nuna cewa Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa ya yafewa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.
A cewar gwamnan ya yafewa mabiyan Sanatan ma. Sannan kuma yi kira ga sanatan da su ajiye duk wata gaba a gefe su zo a tafi tare domin ciyar da jiharsu ta Kano gaba.
Yace: “Na Yafewa Kwankwaso da Mabiyansa 'Yan Kwankwasiyya, don haka ina kira gare su da su zo a tafi tare domin ciyar da jihar Kano gaba.”
A baya Legit.ng ta rahoto cewa yayinda ake shirye-shiryen zaben 2019, manyan masu ruwa da tsaki sunyi yunkurin nuna goyon bayansu ga yan takara uku daga yankin arewa maso yamma don ganin sun lashe kujerar shugabancin kasa.
KU KARANTA KUMA: IMF: Za mu iya biyan duk bashin da ke kan mu – Ministar kudi
Manyan yan siyasan na shirin goyon bayan wadannan shugabanni na arewa da suka hada da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, Sanata Rabiu Kwankwaso da kuma wani tsohon ministan ayyuka na musamman, Turaki Tanimu.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng