Duk mai hankali ya san akwai bukatar mu canja canji a jihar Kano - Kwankwaso

Duk mai hankali ya san akwai bukatar mu canja canji a jihar Kano - Kwankwaso

Wakilin al’ummar Kano ta tsakiya a majalisar dattawan Najeriya, kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi barazanar kawar da gwamnan jihar Kano, Abdullahi Gandue, kamar yadda Legit.ng ta jiyo.

Kwankwaso ya bayyana haka ne a wata ganawa da yayi da masoya da magoya baya a ranar Laraba 30 ga watan Mayu, inda yace ya zama wajibi kowannensu ya amshi katinsa na kada zabe.

KU KARANTA: Kotu ta kama wani tsohon gwamna da laifuka 6 da suka danganci karkatar da kudaden al’umma

“Ga duk mai hankali ya san akwai bukatar canza canji a jihar Kano, don haka ya zama wajibi akan kowa ya je ya amshi katinsa na kada zabe daga hukumar zabe ta kasa, ana nan ana rabawa.” Inji Kwankwaso.

Duk mai hankali ya san akwai bukatar mu canja canji a jihar Kano - Kwankwaso
Ganduje da Kwankwaso

Idan za’a tuna Sanata Kwankwaso ne ya yi ruwa ya yi tsaki don ganin gwamna Ganduje ya kai labari a zaben shekarar 2015, a lokacin da Gandujen ke rike da mukamin mataimakin gwamanan jihar Kano.

Sai dai dangantaka ta yi tsami ne tsakanin Kwankwaso da Gandujen ne jim kadan bayan Kwankwaso ya mika masa ragamar mulki, inda Gandujen ya bayyana cewa Kwankwaso na so ne ya dinga juya shi daga waje, abinda shi kuma ba zai lamunta ba.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng