Jiragen yakin Isra'ila sun sake kai mummunan hari Zirin Gaza

Jiragen yakin Isra'ila sun sake kai mummunan hari Zirin Gaza

Jiragen saman yaki na kasar Isra'ila sun sake kai wani mummunan harin sama na ruwan bama-bamai a yankin zirin gaza wanda Yahudawa suka zagaye a yanzu

Jiragen yakin Isra'ila sun sake kai mummunan hari Zirin Gaza
Jiragen yakin Isra'ila sun sake kai mummunan hari Zirin Gaza

Jiragen saman yaki na kasar Isra'ila sun sake kai wani mummunan harin sama na ruwan bama-bamai a yankin zirin gaza wanda Yahudawa suke zagaye da yankin a yanzu. Jiragen yakin wadanda basu da matuka na kasar ta Isra'ila sun kai hare-haren ne na bama-bamai guda uku a yankin Al-Idaratulmadina. Sannan kuma sun sake kai wani sabon harin sansanin 'yan kungiyar Hamas, wadanda suke dauke da makaman Izzeddin Kassam.

DUBA WANNAN: Za a caji Ramos Pounds biliyan 1, saboda dukan Mohammed Salah da yayi

Sannan kuma rahoto yazo cewar jiragen yakin sun sake kai wani sabon harin akan wasu gonaki da suke yankin AL-Zaitun dake yankin Zirin Gaza.

Majiya mai karfi sun shaida afkuwar lamarin, inda suka ce sojojin kasar ta Isra'ila ma da suke gewaye da yankin sun shaida kai harin.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng