Hukumar Soji ta kama muggan makamai da aka makare cikin wata kwantena a jihar Ogun
- Najeriya dai kowa keson shigo da makamai yana iya kawo abinsa
- Kashe-kashe sunyi yawa a fadin kasar nan
- Kashe-kashen na da alaka da fashi da makami, kisan gilla da na kare dangi
Hukumar Sojin Najeriya, tayi sa'ar kama wata kwantena maqare pal da makamai a kan hanyarta ta zuwa wurin wadanda ke shigo da makamai ba bisa ka'ida ba.
An kama kwantenar ne a kan titin Igunwa Road, kauyen Balogun a jihar Ogun, sai dai ba'a san inda makaman suka nufa ba.
Watakil da an bari an kai makaman inda aka niyyar kaisu da an yi sa'ar kama wasu makaman da ma masu safarar tasu cikin tsanaki, a irin abin da ake kira sting operation.
Sai dai sojin sunyi hanzarin bada labarin kamun nasu, inda aka kuma dauki hotuna na alburusai da aka gani a cikin kayan, da ma bindigogi da ake sa rai 'yan fashi za'a sayar wa.
DUBA WANNAN: Wasu batutuwan cikin zantukan Buhari zuki ta malle ne
A badi dai za'a shiga zaben 2019, kuma ana sa rai wannan karon, kamar dai yadda aka saba a arewa, zabukan zasu zo cike da takaddama da matsuwar ko inci ko a mutu, kamar yadda 'yan siyasa kanyi da yaran talakawa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng