Ku dauko mana kofin Duniya – Shugaba Buhari ga yan kwallon Super Eagles
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga tawagar yan kwallon Najeriya da zasu wakilci kasar a gasar cin kofin Duniya da zai gudana a kasar Rasha, Super Eagles da su tabbata sun ciyo ma Najeriya kofin, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.
Buhari ya bayyana haka ne a yayin da ya karbi bakoncin tawagar yan kwallon kafar a fadar gwamnati dake Abuja a ranar Laraba, 30 ga watan Mayu, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
KU KARANTA: Yansanda sun bankado wasu tarin makamai a wata kamfanin kera makamai dake Benuwe
An gudanar da taron ne kafin a fara taron majalisar zartarwa, inda shugaban ya bayyana yan wasan a matsayin matasa, masu karfi a jika, don haka ya basu shawarar su yi amfani da damarsu wajen lallasa abokan karawarsu.
Daga cikin wadanda suka halarci zaman akwai Ministan wasanni, Solomon Dalung, mai horas da kungiyar, Gernot Rohr, da kafatanin yan wasan Najeriya guda 24 da zasu wakilci Najeriya Rasha.
Tawagar za ta wuce kasar Ingila a ranar Laraba, 30 ga watan Mayu don shirin fafatawa da kasar Ingila a wasan sada zumunta da zasu buga a ranar Asabar, 2 ga watan Yuni, a babban filin wasa na Wembley.
Bayan kammala wasansu a kasar Ingila, tawagar za ta zarce garin Tatzmannsdorf dake kasar Austria, inda zata kwashe kwanaki takwas tana atisaye, inda zata kara a wasan sada zumunta da kasar Czech republic, daga nan kuma za ta wuce kasar Rasha.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng