Abin kunya: An gurfanar da wani saurayi da ya yi wa budurwarsa sata a gaban kuliya

Abin kunya: An gurfanar da wani saurayi da ya yi wa budurwarsa sata a gaban kuliya

A yau Laraba ne wata kotun Abuja da ke zamanta a Garki Abuja ta yanke wa wani Elvis Anthony mai shekaru 34 hukuncin watanni biyar a gidan kurkuku saboda satar kudade da wayar salular budurwarsa.

Sai dai Alkalin kotun, Inuwa Maiwada ya bawa Anthony zabin biyan tarar N5,000.

Kotun kuma ta sake samun Mr Anthony da ke zaune a Aso Pada, Mararaba a jihar Nasarawa da laifin sata.

KU KARANTA: Dakarun sunyi wa wasu barayin danyen mai laga-laga bayan musayar wuta mai zafi

Wanda ake tuhumar ya amsa laifinsa inda ya roki kotun tayi masa sassauci wajen yanke hukunci. Ya kuma kara da cewa wanda ya yi wa satar budurwarsa ne har ma an sa musu ranar aure.

Abin kunya: An gurfanar da wani saurayi da ya yi wa budurwarsa sata a gaban kuliya
Abin kunya: An gurfanar da wani saurayi da ya yi wa budurwarsa sata a gaban kuliya
Asali: UGC

Tun da fari, mai shigar da kara, Ifeoma Ukahga ya shaidawa kotu cewa wata Ene Ugah da ke zama a Nyanya Abuja ne ya shigar da kara a caji ofis da ke Utako a Abuja a ranar 20 ga watan Fabrairun 2018.

Ta ce Mr Anthony ya damfari wanda ta shigar da karar ne ta hanyar kai ta K City Plaza da ke Wuse Abuja don ta yi siyaya, amma lokacin da ta ke sayayar sai wanda aka gurfanar da sace mata N240,000 tare da wayar salula kirar Infinix Hot wanda kudinsa ya kai N45,000.

Mai shigar da karar ya ce wanda ake yanke wa hukuncin ya tsere tun ranar da ya yi satar ba'a sake ganinsa ba sai rannan 20 ga watan Mayu da aka kama shi.

Ta ce ya amsa laifinsa yayinda da ake masa tambayoyi kuma ya roki ayi masa gafara.

Laifin da ya aikata ya sabawa sashi na 288 na Penal Code.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164