Yansanda sun bankado wasu tarin makamai a wata kamfanin kera makamai dake Benuwe

Yansanda sun bankado wasu tarin makamai a wata kamfanin kera makamai dake Benuwe

Rundunar Yansandan jihar Benuwe ta kama wani Uba da dansa masu sana’ar kira da suka shahara wajen kera muggan makamai, suna ruruwa wutar rikicin dake ci a jihar Benuwe garin a Oju dake cikin karamar hukumar Oju na jihar, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito

Kaakakin rundunar Yansandan jihar, ASP Joel Yamu ne ya tabbatar da kamen, inda yace baya da kama Odah Abi, da dansa Kinsgley Abi, Yansanda sun cafke wani abokin Abi mai suna Ode Thomas, kuma yace sun samu nasarar kama su ne a yayin bincike da suke yi kan zargin yi ma wata budurwa fyade da Ode Abi yayi.

KU KARANTA: Tura ta kai bango: Sarkin Musulmi ya yi kaca kaca da gwamnan jihar Benuwe da wani tsohon Minista

Yansanda sun bankado wasu tarin makamai a wata kamfanin kera makamai dake Benuwe
Uba da Da da Abokinsa

Daga cikin makaman da aka kama a hannun mutanen akwai:

Bindigar G3

Kwankon alburusai

Karafan kera Bindigu

Gindin bindigu guda 3

Bindigar roba tabar wiwi

Katunan haramtacciyar kwayar Tramadol da sauran kayayyakin da suke amfani dasu wajen kara bindgu dake sauran muggan makamai.

Yansanda sun bankado wasu tarin makamai a wata kamfanin kera makamai dake Benuwe
Makaman

A bayaninsa, Kaakaki Yamu ya bayyana godiyar rundunar Yansanda game da gudunmuwar da jama’an jihar Benuwe ke basu a yaki da suke yi a miyagun ayyuka a fadin jihar gaba daya.

Daga karshe yace zasu cigaba da gudanar da bincike, kuma da zarar sun kammala zasu gurfanar da mutanen gaban Kotu don su fuskanci hukunci.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng