Sheikh Dahiru Bauchi ya kafa tarihi 4 a duniyar tafsirin Al-qur'ani mai girma

Sheikh Dahiru Bauchi ya kafa tarihi 4 a duniyar tafsirin Al-qur'ani mai girma

Mun samu daga majiyar mu ta Rariya cewa shahararren malamin nan, shugaban mazhabar darika a Najeriya kuma fitaccen mai tafsirin al'qur'ani mai girma Sheikh Dahiru Bauchi ya zama gagarabadau a duniyar tafsiri biyo bayan wasu muhimman tarihai da ya kafa a fagen har uku.

Malamin dai yana bin salon Tafsirin Al-qur'ani ne da tsari na fassara Kur'ani da Kur'ani, fassara Kur'ani da Hadisin Manzon Allaah SallalLaHu AlaiHi Wa AliHi Was Sallam, fassara Kur'ani da maganganun Sahabai da Tabi'ai da magabatan Bayi na kwarai.

Sheikh Dahiru Bauchi ya kafa tarihi 4 a duniyar tafsirin Al-qur'ani mai girma
Sheikh Dahiru Bauchi ya kafa tarihi 4 a duniyar tafsirin Al-qur'ani mai girma

KU KARANTA: Ruwa yayi ajalin wani Alaramma a jihar Gombe

Kamar dai yadda muka samu, a bana ne fitaccen malamin Sheikh Dahir Usman Bauchi da ke zama a garin Kaduna ya cika shekaru 67 yana gabatar da Tafsirin Alqu'ani.

Ya fara Tafsirin Kur'ani a watan Ramadan na Shekarar 1951.

Haka mai dai kuma a wannan azumin na bana ne Sheihin Malamin ya cika shekaru 54 yana gabatar da Tafsirin Al-qur'ani da ka ba tare da duba takarda ba.

Wani tarihin da shehin malamin ya kara kafawa kuma shine a bana ya cika shekaru 39 yana tafsirin al'qur'ani mai girma a Birnin Kaduna.

Haka ma dai kamar yadda muka samu daga majiyar ta mu, fitaccen malamin a wannan shekarar ne ake sa ran zai yi tafsirin Al-qur'ani mai girma har sau uku a rayuwar sa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng