Dandalin Kannywood: Jarumin jarumai Adam Zango ya amsa kirar fadar shugaban kasa (Hotuna)
A iya cewa sakamakon suna da fitaccen jarumin fina finan Kannywood, Adam Zango yayi biyo bayan muhimmin rawar da yake takawa a fagen shirin fina finan Hausa, haka ya sanya idanun jama’a ya koma kansa, inda a dalilin haka ya samu karbu a ciki da wajen Najeriya.
Legit.ng ta ruwaito a daren ranar Talata, 29 ga watan Mayu ne aka hangi jarumin Gwaska, Adam a wani babban taro da fadar shugaban kasa ta shirya, inda aka hange shi yana gaisawa da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.
KU KARANTA: Mutane da dama sun mutu a wani arangama tsakanin yan bindiga da kauyawa Zamfara
Fadar shugaban kasa ta shirya wannan liyafar ne a bikin murnar zagayowar ranar Dimukradiyya na shekarar 2019, inda aka gayyaci fitattun jaruman fina finan Hausa da na Turanci.
A yayin wannan taro, mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ya jagoranci manyan jami’an gwamnatin Najeriya wajen yanka kek na murnar cikar Najeriya shekaru 19 akan turbar Dimukradiyya.
A wani labarin kuma, Hausaw mazauna birnin Paris, babban birnin kasar Faransa sun gayyaci Zango zuwa kasar Faransa don gabatar da wasa a murnar nadin wasu shuwagabannin Hausawan kasar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng