Mutane da dama sun mutu a wani arangama tsakanin yan bindiga da kauyawa Zamfara

Mutane da dama sun mutu a wani arangama tsakanin yan bindiga da kauyawa Zamfara

A ranar Talata 29 ga watan Mayu ne wasu gungun yan bindiga suka kai farmaki wani kauye dake cikin karamar hukumar Tsafe na jihar Zamfara, inda aka samu asarar rayuka daga kowanne bangare, inji rahoton Legit.ng.

Wani dan asali garin Tsafe, kuma ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Abubakar Balarabe Ibrahim Chafe ne ya tabbatar da wannan hari a shafinsa, inda yace yan bindigar sun kai farmakin ne a kauyen Gangami, dake cikin Tsafe.

KU KARANTA: Kyan kai: Atiku Abubakar zai gina kafataren Asibiti a babban birnin tarayya Abuja

Sai dai da yake karin haske, Ibrahim yace yan bindigar sun gamu da fushin mutanen kauyen, inda suka yi fito na fito dasu, wanda ta kai ga an samu asarar rayuka daga bangaren yan bindigar, da kuma jama’an kauyen.

Matsalar hare haren yan bindiga na nema ya zama ruwan dare a jihar Zamfara da kewayenta, inda tun a shekarar da ta gabata ne yan bindiga ke cin karensu babu babbaka a jihar, inda suka kashe daruruwan mutane, ciki har da yara da mata.

Sai dai a kwanakin baya ne dai aka hallaka tsohon gawurtaccen shugaban yan bindigar jihar Zamfara, Buharin Daji, wanda ya gamu da ajalinsa a hannun wani tsohon yaronsa, Dogo Gide. Sai dai tun bayan mutuwar Buhari, hare hare sun yi kamari daga yaransa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel