Allah daya gari bambam:Yadda wata kabila a Arewacin Najeriya ke ganawa da aljanu kafin su fara noma

Allah daya gari bambam:Yadda wata kabila a Arewacin Najeriya ke ganawa da aljanu kafin su fara noma

Akwai wani wasu mutanen wata kabila dake jihar Filato dake gudanar wa wani shagali a duk lokacin da damuna ta fadi a shirye shiryensu na kaddamar da noma, inda a yayin wannan bikin, suna kashe mutum, kuma ya tashi da ransa.

Gidan rediyon Muryar Amurka ta ruwaito sunan kabilar, Lur, tana cikin karamar hukumar Kanke na jihar Filato, inda kafatanin mutanen garin maza da mata, yara da kanana ke fita a karkashin jagorancin Sarkin garin don halartar wannan taron, ana kida ana shewa ana rawa

KU KARANTA:BBahaushe mai ban haushi: Uwargida ta maka Uban ýaýanta gaban Kotu kan watsi da yaransu

Sarkin garin, Nde Ridak James Nendak ya bayyana ma majiyar Legit.ng cewa sun saba yin wannan al’ada shekara da shekaru, a yayin bikin ana daura wani matashi a wuyan wasu kartai, inda zai bi gida gida yana amso irin dawa.

Bayan ya amso irin, za’a kawo shi tsakiyar taro nana masa kida yana rangaji daga wuyan kartan, daga nan sai ya sauko ya tafi kusa da wani dutse da ake kira Lipdal, sai ya daura dawar akan dutsen, nan take zai fadi matacce.

Sai dai bayan wani dan lokaci wasu aljanu zasu taro akan dutsen, inda zasu dauki geron, idan har za’a samu noman dawa mai kyau a shekarar, zasu ajiye irin dawar, sai matashin ya tashi da ransa daga mutuwar da yayi, sai ya dauki irin dawar, a cigaba da kida ana shewa, daga nan duk manomi zai iya wuce gonarsa ya fara noma, kamar yadda Ciroman garin, Danlami Barce ya tabbatar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel