‘Yan Boko haram sun kaiwa makiyaya hari, an yi asarar rai da dukiya

‘Yan Boko haram sun kaiwa makiyaya hari, an yi asarar rai da dukiya

A kalla mutun guda ne ya mutu tare da sace shanun da ba a san adadin su ba bayan wasu da ake kyautata zaton mayakan kungiyar Boko Haram ne suka kaiwa wasu makiyaya hari a jihar Borno.

Maharan, da ake zaton ‘yan Boko Haram ne, sun kaiwa makiyayan hari ne a dajin Pumbum na karanmar hukumar Askira Uba dake kudancin jihar Borno.

Lamarin ya faru ne ranar Litinin da yamma, amma labara bai iso zuwa cikin garin Maiduguri mai nisan kilomita 170 daga Askira ba sai safiyar yau, Talata.

‘Yan Boko haram sun kaiwa makiyaya hari, an yi asarar rai da sace shanu
‘Yan Boko haram sun kaiwa makiyaya hari

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Damian Chukwu, ya tabbatar da afkuwar lamarin tare da bayyana cewar har yanzu hukumar ‘yan sanda bata da masaniyar adadin shanun da aka sace. Saidai ya ce suna cigaba da bincike, kazalika ya bukaci jama’a da su bawa jami’an tsaro hadin kai domin samun sahihan bayanai.

DUBA WANNAN: Tinubu na zawarcin wasu fitattun 'yan Najeriya biyu zuwa jam'iyyar APC

Ya kara da cewar mutum guda da mayakan Boko Haram suka kasha, sun same shi ne a gida yayin da ‘yan uwan sa suka tafi wani masallaci dake Bulumkutu domin yin sallar Isha.

Chukwu y ace jami’an ‘yan sanda sun sami mutumin da aka kasha din kwance cikin jinni a kan gaodon sad a misalign karfe 10:01 na daren ranar Litinin. Ya bayyana sunan wanda aka kashe din da Umar Telka Bulumkutu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng