Ranar Demokaradiyya: Batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo a jawabinsa

Ranar Demokaradiyya: Batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo a jawabinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi jawabi ga ‘yan Najeriya a ranar demokaradiyya, inda ya tunawa ‘yan Najeriya cika shekaru 19 da Najeriya ta dawo turbar yanci.

Wannan rana ta kuma yi daidai da cikar shugaban kasar shekaru 3 akan karagar mulki.

A cikin jawabin nasa, Shuaban kasa Muhammadu Buhari ya tabo wasu muhimman babtutuwa da suka shafi cigaban da kasar ta samu.

Ranar Demokaradiyya: Batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo a jawabinsa
Ranar Demokaradiyya: Batutuwa 5 da Shugaba Buhari ya tabo a jawabinsa

1. Buhari ya yi jawabi kan cewa lallai anci nasarar karya lagon kungiyar Boko Haram a hare haren da take kaiwa a yankinArewa maso gabashin Najeriya. Duk kuwa da cewar Shugaban ya kaucewa bayyana cewar an gama da Boko Haram.

2. Buhari ya bayyana cewa gwamnatinsa tayi nasarar kwato ‘yan matan Chibok 106 da Boko Haram suka sace su, da kuma ‘yan mata 104 da aka ci nasarar kwato su da Boko Haram din suka sace a makarantar ‘yan mata ta Dapchi dake jihar Yobe, da kuma wasu karin mutane 16,000 da aka kwato daga hannun ‘yan Boko Haram.

3. Ya kuma yi Magana kan batun da ya masu yin garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, da kuma batun rikicin da yaki ci yaki cinyewa na tsakanin Manoma da kuma Makiyaya, wanda ya janyo hasarar rayuka masu dumbin yawa musamman a yankin Binuwai da Taraba da Adamawa.

4. Shugaban yayi bayanin yadda aka samu zaman lafiya a yankin Neja Dalta mai arzikin man fetur, inda yace ana samun cigaba wajen samar da zaman afiya a yankin, domin samun adadin man da ake bukata a kullum domin samarwa da Gwamnatin Najeriya kudaden shiga.

5. Shugaban yayi bayanin irin dumbin kudaden da Gwamnati ta tara a tsarin asusun nan na bai daya wato TSA, inda yace anci nasarar tara sama da Naira biliyan 200 wajen kudaden da ake baiwa ma’aikatan bogi, da kuma dawo da zunzurutun kudi Naira biliyan 500 daga hannun masu handama da babakere.

KU KARANTA KUMA: Ku magance matsalar rashin tsaro maimakon ku dorawa wasu laifi – Atiku ga gwamnatin tarayya

Wadannan sune wasu daga cikin jawaban da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ga talakawansa a yau, Talata, 29 ga watan Mayu.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, Gwamnan jihar Niger Abubakar Bello, a ranar Litinin, ya bayyana dalilai da dama wadanda suka nuna cewa ya kamata ‘yan Najeriya su sake jefawa Buhari kuri’a a zaben 2019.

Bello, ya bayyana cewa sake tsayawar Muhammadu Buhari takarar shugaban kasa a 2019, shine domin shimfida kwakwaran tubalin ginin cigaban damokradiyyar Najeriya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng