Hukumar EFCC ta na wala-wala da Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara
- An maka tsohon Gwamnan Jihar Zamfara a gaban Kotu a kan zargin cin kudi
- Ana zargin Mahmud Shinkafi wani tsohon Minista da cin kudi har Miliyan 450
- Kotu ta bada belin wadanda ake zargi an kuma dage shari’a sai bayan wata guda
Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa a jiya ne aka maka tsohon Gwamnan Jihar Zamfara Mahmud Aliyu Shinkafi da kuma tsohon Ministan Kasar watau Bashir Yuguda a gaban Kotu. Ana zargin su da karkatar da Naira Miliyan 450.
Hukumar EFCC mai yaki da barayi tana karar tsohon Gwamnan na Jihar Zamfara tare da wani Minista a lokacin Gwamnatin Jonathan Bashir Yuguda a babban Kotun Tarayya da ke Garin Gusau a Jihar Zamfara da wasu manyan laifuffuka 5.
Sauran wadanda ake zargi da wannan laifi sun hada da Alhaji Aminu Nahuche da kuma wani Alhaji Ibrahim Mallaha. Ana zargin wadannan mutane da cin wasu makudan Miliyoyin kudi ba tare da yin aikin kobo guda ba a shekarun baya.
KU KARANTA: An gano yadda Shugabannin Najeriya ke lamushe dukiyar Gwamnati
Wadanda dai ake tuhuma sun bayyanawa Kotu cewa ba su aikata laifin da ake zargin su da shi ba. Alkali mai shari’a Fatima Murtala Aliyu ta bada belin wadannan mutane dukka inda ta nemi a bada jinginar kudi Naira Miliyan 5 a Kotu.
Bayan nan kuma an karbe takardun su na fita kasashen waje inda aka daga shari’ar. Yanzu dai Alkalin ta sa rana za a koma gaban Kotu ne a karshen watan Yuni. Kwanaki dai tsohon Gwamna Mahmud Shinkafi ya bar PDP ya dawo APC.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng