‘Yan sanda sun yiwa wata mata mai gemu zigidir domin tabbatar da jinsin ta

‘Yan sanda sun yiwa wata mata mai gemu zigidir domin tabbatar da jinsin ta

Wata mata, Teresiah Mumbi, ta yi barazanar gurfanar da wasu ‘yan sanda biyu dake Nairobi, a kasar Kenya, bisa yi mata tsirara domin tabbatar da jinsin ta don kawai tana da gemu.

Mumbi, mai shekaru 31 a Duniya ta shaidawa wata jaridar kasar Kenya, Myjoyonlie, cewar ,yan sanda sun fara kama ta a kan laifin karya dokar tuki amma suka tilasta mata yin zigidir domin tabbatar da cewar ita mace ce saboda tana da gemu a fuskar ta.

‘Yan sanda sun yiwa wata mata mai gemu zigidir domin tabbatar da jinsin ta
‘Yan sanda sun yiwa wata mata mai gemu zigidir domin tabbatar da jinsin ta

Da take Magana da wani gidan talabijin din kasar Kenya, KTN Televcision, matar ta bayyana cewar wasu ‘yan sanda mata biyu ne suka bukaci tantance jinsin ta bayan ta bayyana ita mace ce.

Yan sanda biyu mata sun bukaci na tube kaya na tare da bude kafafu na. Amma ko bayan sun gamsu cewar ni mace ce sai suka mayar da ni suka garkame,” a cewar Mumbi.

DUBA WANNAN: Mayakan kungiyar Boko Haram 132 sun mika wuya ga dakarun soji, sun ajiye makan su

Mumbi ta bayyana cewar ta daina aske gemun ta ne saboda kaikayi dake hanata sakat duk lokacin da ta cire gemun. Sannan ta kara da cewa ta bar aiki bayan ta daina aske gemun.

Jami’ar ‘yan sanda, Alice Kimeli, dake Huruma bata tabbatar da labarin Mumbita ba, domin lokacin da aka tuntube ta, t ace tana halartar wani taro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel