Yanzu Yanzu: Osinbajo ya gana da Saraki, Kwankwaso da ‘yan sabuwar PDP

Yanzu Yanzu: Osinbajo ya gana da Saraki, Kwankwaso da ‘yan sabuwar PDP

Mataimakin shugaban kasa, Ferfesa Yemi Osinbajo ya gana da jiga-jigan sabuwar PDP a yau Litinin, 28 ga watan Mayu.

Shugaban majalisar dattawa ne ya jagoranci mambobin sabuwar PDP zuwa wajen ganawar wanda ya gudana a gidan mataimakin shugaban kasar wato Aguda wanda ke fadar shugaban kasa.

Inda mataimakin shugaban kasa kuma ya jagoranci tawagar gwamnati. Sunyi ganawar ne a cikin sirri.

Mambobin sabuwar PDP da suka halarci zaman sun hada da Sanata Kwankwaso dan majalisar dattawa mai wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattawa, Aminu Waziri Tambuwal, Yakubu Dogara, Kawu Baraje, Abdulfatai Ahmed na Kwara, Murtala Nyako, Barnabas Gemade, Danjuma Goje da sauran gaggan mutanan da suka balle suka kafa jam’iyyar APC.

Tawagar gwamnati kuma sun hada da mataimakin shugaban jam’iyyar APC shiyar Arewa, Lawal Shuaib, Ministan shari’a, Abubakar Malami, mataimakin shugaban ma’aikata na shugaban kasa, Ade Ipaye, da kuma kakakin mai ba kasa shawara a harkar tsaro, Babaguno Monguno.

Yanzu Yanzu: Osinbajo ya gana da Saraki da Kwankwaso da ‘yan sabuwar PDP
Yanzu Yanzu: Osinbajo ya gana da Saraki da Kwankwaso da ‘yan sabuwar PDP

Idan za’a iya tunawa a ranar Lahadin da ta gabata jagoran ‘yan sabuwar PDP Kawu Baraje a birnin Ilori, ya bayyana cewa zasu gana da mataimakin Shugaban kasa domin tattaunawa saboda a kawo karshen turka turkar da ake fama da ita tsakanin ‘yan sabuwar PDP din da kuma bangaren ‘yan APC din.

KU KARANTA KUMA: Zargin cin hancin N17bn: Okonjo-Iweala ta kalubalanci Gbajabiamila

Baraje ya bayyana cewar, yana fatan a karshen tattaunawar da za’a yi tsakanin bangarorin biyu ta zama mai ma’ana kuma ta haifar da da mai ido, domin cigaban jam’iyyar ta APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel