Cristiano Ronaldo na kokarin komawa Kungiyar Manchester United

Cristiano Ronaldo na kokarin komawa Kungiyar Manchester United

Mun samu labari cewa fitaccen ‘Dan wasan Kasar Portugal Cristiano Ronaldo na shirin barin Kungiyar Real Madrid. ‘Dan wasan na kokarin dawowa tsohon Kungiyar sa watau Manchester United.

'Dan wasa Cristiano Ronaldo mai shekaru 33 na iya barin Real Madrid ne ya dawo Kasar Ingila a kakar bana kamar yadda’Yan jaridun Kasar Sifen Diario Gol su ke rahotowa. Diario Gol yace Ronaldo na kokarin dawowa Manchester United.

Cristiano Ronaldo na kokarin komawa Kungiyar Manchester United
Manchester United da PSG na neman Cristiano Ronaldo

Tun ba yau ba dai Kungiyar Manchester United ta ke zawarcin ‘Dan wasan na Duniya. A 2013 dai Manchester United ta sa rai tsohon ‘Dan wasan na ta zai dawo. A 2015 ma dai an yi tunani Ronaldo zai bar Real Madrid ya dawo Kasar Ingila.

KU KARANTA: Amurka ta koro wani 'Dan Najeriya saboda latsa yarinya

Kwanakin baya ‘Dan wasan gaban ya nuna cewa zai bar Real Madrid sai kuma aka kara masa albashi. Watakila dai wannan karo ma ‘Dan wasan ya samu karin albashi a Kungiyar. Haka kuma irin su PSG na neman babban ‘Dan wasan na Duniya.

Kwanakin baya dai kun ji cewa PSG na iya saida Neymar zuwa Real Madrid. Hakan na iya sa shi kuma Ronaldo ya bar Real Madrid bayan yayi shekaru kusan 10 yana buga kwallo a Sifen.

A makon nan ne dai aka buga wasan karshe na Zakarun Nahiyar Turai tsakanin Madrid da Liverpool. Real Madrid ta kafa tarihi a Duniya bayan doke Liverpool din da ci 3-1 a wasan karshe.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel