Kannywood: Ali Nuhu ziyarci Moda ziyara, yace yana murmurewa

Kannywood: Ali Nuhu ziyarci Moda ziyara, yace yana murmurewa

Shahararren jarumin nan na kamfanin shirya fina-finan Hausa, Ali Nuhu wanda aka fi sani da sarki mai sangaya da Kannywood ya ziyarci Sani Moda a asibitin da yake jinya.

Ali ya ziyarci tsohon abokin aikin nasa ne dake fama da jinya a asibitin da yake kwance na garin Kaduna.

Ya sanar da hakan ne a shafin sa na kafafen sada zumunta tare da rubuta cewa "Alhamdulillah Sani Idris Moda yana kara samun lafiya.

Bisa ga wannan sabuwar sanarwa da yayi, abun farin ciki ne ga dinbim mabiyan jarumai da fina-finan hausa ta Kannywood bayan ga jita-jitan da ya yadu kwanan baya cewa jarumin ya rasu.

Kannywood: Ali Nuhu ziyarci Moda ziyara, yace yana murmurewa
Kannywood: Ali Nuhu ziyarci Moda ziyara, yace yana murmurewa

Idan bazaku manta ba a kwanakin baya ana ta yada jita-jitan mutuwar tsohon jarumin na Kannywood wato Moda.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Shehu Sani ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar gwamna a jihar Kaduna

Sai dai Moda ya karyata jita-jitan inda ya bayyana ma jaridar Rariya cewa yana nan da ran shi bai mutu ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel