Tsohon Shugaban Kasa Jonathan yace shi ya kirkiro tsarin BVN da Buhari yake ji da shi

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan yace shi ya kirkiro tsarin BVN da Buhari yake ji da shi

- Tsohon Shugaban kasa Jonathan yace shi ya kawo tsarin nan na BVN

- Gwamnatin Buhari ce ta dabbaka wannan tsari domin maganin barayi

- Jonathan din ya dai lissafo kadan daga cikin ayyukan da yayi a mulki

Jiya mu ka ji labari cewa tsohon Shugaban Kasar nan Dr. Goodluck Jonathan ya bayyana cewa sai da ya kammala ayyuka sama da 1000 a lokacin da yake rike da Kasar nan tsakanin 2010 zuwa 2015.

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan yace shi ya kirkiro tsarin BVN da Buhari yake ji da shi
Tsohon Shugaban kasa Jonathan yace da bazar sa APC ta ke rawa

Tsohon Shugaban Kasa Jonathan ta bakin Mai ba sa shawara kan kafofin sadarwa na zamani a wancan lokaci Reno Omokri yace sai da ya kirkiri fiye da ayyuka 1000 kuma ya kammala su sarai a lokacin mulkin sa wanda daga ciki akwai tsarin BVN.

KU KARANTA: Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya yabawa aikin Fayose

A jawabin na tsohon Shugaban kasar ya hada da yi wa Adams Oshiomole raddi bayan ya zargi Gwamnatin sa da satar dukiyar Kasa. Jonathan yace shi ya gyara filin jirgin sama na Garin Enugu ya kuma kirkiro sababbin Jami’o’i har 12.

Bayan nan Jonathan yace daga cikin ayyukan sa akwai gina Makarantun zamani na Almajirai da kuma kawo tsarin You Win da GIS domin Matasa. Har wa yau Jonathan yace shi ya kawo wasu hanyoyin dogo da kuma tituna a Kasar.

Duk da kiran tsohon Shugaban barawo, Omokri yace gidajen da tsohon Gwamnan Edo Adams Oshiomole ya gina sun fi na Jonathan kyau, duk da cewa Jonathan din ya rike Najeriya kuma kafin nan ya rike kujerar Gwamnan Jihar Bayelsa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng