Zaben 2019: Atiku ya naɗa wani tsohon gwamna a matsayin shugaban yakin neman zabensa
Tun a baya ne dai alamu suka tabbatar da cewa tsohon mataimakin shugaban kasa daga shekarar 1999 zuwa 2007, Alhaji Atiku Abubakar zai sake tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2019, da nufin neman darewa kujerar lamba ta daya a Najeriya.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito shirye shirye sun fara kankama na ganin tsohon mataimaki Atiku Abubakar ya kai labari a zaben shekarar 2019, inda zuwa yanzu har ya nada wani tsohon gwamna a matsayin jagoran yakin neman zabensa.
KU KARANTA: Yansanda sun kwato sandar ikon majalisar Dokokin jihar Gombe da yan majalisar suka sace
Gidan talabijin na TVC ta ruwaito wannan jagora na yakin neman zaben Atiku ba wani bane illa tsohon gwamnan jihar Ogun, Otunba Gbenga Daniel, da ya mulki jihar daga shekarar 2003 zuwa 2011.
Cikin wata wasika da ta samu hannun sa hannun Atiku, wanda majiyarmu ta gani Atiku ya bayyana nauyin da suka rataya a wuyar Daniel sun hada da kula da ma’aikata, samar da kudi da kuma zabo mutanen da zasu yi yakin neman zaben.
Atiku ya bayyana Daniel a matsayin kwararren Injiniya, dan kasuwa kuma dan siyasa, haka zalika mutum ne dake ilimin siyasar Najeriya mai jama’a a dukkanin bangarorin kasar nan, inji Atiku.
Daga karshe Atiku ya bayyana cewa Daniel zai dinga bashi rahoton ayyukansu kai tsaye, kamar yadda wani shafin magoya bayan Atiku ‘Youth for Atiku’ dake Twitter suka tabbatar.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng