Shugaba Buhari ya bayyana nasarorin da Gwamnatin sa ta samu shekarar da ta wuce

Shugaba Buhari ya bayyana nasarorin da Gwamnatin sa ta samu shekarar da ta wuce

- Shugaban kasa Buhari ya fadi kadan daga cikin aikin wannan Gwamnati

- Yanzu dai Najeriya ta rage dogaro da arzikin man fetur domin samun kudi

- An samu karuwar kayan da Najeriya ta ke fita da su zuwa Kasashen waje

A jiya ne Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari ta zayyano wasu kadan daga cikin gaban da aka samu a karkashin mulkin APC a bangaren tattalin arziki a shekarar da ta wuce ta 2017 a shafukan sadarwa na zamani na Fadar Shugaban Kasa.

Shugaba Buhari ya bayyana nasarorin da Gwamnatin sa ta samu shekarar da ta wuce
Alkaluma daga NigerianStat sun nuna akwai cigaba a Najeriya

Fadar Shugaban Kasar ta bayyana cewa an samu karuwar kayan da Najeriya ke fita da su kasashen ketare a Gwamnatin Buhari. Alkaluma sun nuna cewa a bara kurum an samu nunkuwar yawan kayan amfanin gona da Najeriya ke fita da shi waje.

Haka kuma dai idan aka zo kan ma’adanai za a ga cewa abin da Najeriya ta ke fita da shi waje a da kafin zuwan wannan Gwamnati ya nunku da kashi 5 zuwa 6. Hakan dai na nufin Najeriya na rage dogaro da karfin man fetur domin samun kudin shiga.

KU KARANTA: Buhari ya soke wata kwangila da aka ba Yahudawa

Shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa har kayan da Najeriya ta kera a gida yanzu sun fara fita waje fiye da yadda lamarin yake a baya. A bara an samu karuwar kashi 26.8% na kayan da aka kera a Najeriya da su ka bar gida zuwa Kasashen waje.

Kamar yadda ku ka samu labari kwanaki, Kamfanin nan na Ajaokuta na daf da fara aiki bayan shekara da shekaru. Wani babban Jami’in kamfanin yace bayan an yi shekaru 40 ba a kera ko cokali ba ana sa rai Ajaokuta ta tashi a Gwamnatin nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng