Goodluck ya roki Gwamnatin Shugaba Buhari ayi zaben kwarai a Ekiti
Mun samu labari cewa a jiya ne tsohon Shugaban Kasar nan watau Dr. Goodluck Ebele Jonathan da wasu manyan Jam’iyyar PDP su ka shiga Jihar Ekiti domin kaddamar da wani aiki na Gwamna Ayo Fayose kuma su kayi wa PDP kamfe.
Tsohon Shugaba Goodluck Jonathan da wasu Gwamnonin Jam’iyyar PDP irin su Gwamna Nyesom Wike na Jihar Ribas da Ibrahim Hassan Dankwambo na Gombe su na Garin Ado-Ekiti babban Birnin Jihar Ekiti a karshen makon nan.
Goodluck Jonathan ya je ne domin kaddamar da wani titin sama da Gwamna Ayo Fayose ya kammala. Wannan dai shi ne karo na farko da aka samu irin wannan titi a kaf Jihar Ekiti don haka Jonathan ya jinjinawa Gwamnan mai barin gado.
KU KARANTA: Ko ‘Yan N-PDP na iya takawa Shugaban kasa Buhari burki a 2019?
A wajen kaddamar da wannan hanya, Jonathan yace kaf Kasar nan babu titin da ya kai irin wanda Gwamna Fayose ya gina a yanzu. Jonthan yace har a Legas da ma Birnin Tarayya Abuja ba za a samu kamar irin wannan titi da Fayose ya gina ba.
Bayan titin mai tsawon kilomita 1.3, Gwamna Ayo Fayose ya kuma kaddamar da sabon gidan Gwamnatin Jihar. Dr. Goodluck ya roki Gwamnatin Shugaba Buhari ta bari ayi zaben kwarai a Ekiti inda za a kara har da Ministan Shugaba Buharin.
Kwanaki kun ji cewa Mataimakin Majalisar Dattawa Ike Ekeremadu da Gwamnan Jihar Ribas din Nyesome Wike da shi Gwamnan Jihar Ekiti Ayo Fayose sun halarci wurin bikin kaddamar da littaffin da Paul Nwankwo ya rubuta kan tarihin Jonathan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng