2019: Abubuwan da shugaba Buhari yayi a watanni 36 tun hawansa mulki - Aso Rock
- Shugaba Buhari ya hau mulki a 2015, bayan ya wahala shekaru 12 kan nema
- A yanzu yana neman wa'adi na biyu duk da ya tsufa
- Malaman siyasa daga Aso Rock sun zayyana ayyukan da yayi
A wannan mako mai kamawa ne, Najeriya zata cika shekaru 19 kan turbar dimokuradiyya, tun bayan da aka bar tsarin soji na danniya, kuma gwamnatin Tarayya ta sake ware kwanakin hutu har hudu don a tuna baya, a kuma sha biki.
A zayyanar da fadar Aso Rock ta bayar, tace a mulkin shugaban, an sami ci gaba sosai tun daga 2015 ya zuwa yanzu, inda aka sami kama kudaden haram da aka handame, tara kudin gwamnati a waje daya watau TSA, da ma zubo manyan ayyuka a ko'ina a fadin kasar nan.
DUBA WANNAN: A makon nan najeriya zata balle - Biafra
Sai batun ceto jihohi daga uban bashin da suka fada, nan ma fadar tace shugaban yayi rawar gani. Sun kuma tabo batun ciyar da dalibai da ma batun sufuri.
Ummul aba'isin kuma harkar noma, inda gwamnatin tace ta farfado da noma da baiwa samari ayyukan yi da taimakon marasa galihu da dan na cefane.
A karshe, gwamnatin ta tabo batun tsaro, inda tace tana kan ganiyar murkushe Boko Haram, da samar da ayyukan yi da matsugunnai ga wadanda abin ya shafa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng