An damke soji 2 da wasu 13 da laifin fashi da makami

An damke soji 2 da wasu 13 da laifin fashi da makami

- Hukumar yan sanda sun damke wasu mambobin daban fashi da makami a jihar Oyo

- Daga cikinsu akwai jami'in sojan kasa daya da kuma na ruwa daya

Hukumar yan sandan jihar Oyo, ta damke mutane 15 wadanda suke mambobin kungiyar yan fashi da suka addabi jihar Oyo.

Daga cikin wadanda aka kama sune jami'in sojan ruwa mai suna, Jimoh Adesoye, da kuma wani sojan kasa.

Kwamishanan yan sandan jihar, Abiodun Odude, yayinda suka bayyana yan fasin wajen an damke jami'in sojan ne da mambobi 12 da daban.

An damke soji 2 da wasu 13 da laifin fashi da makami
An damke soji 2 da wasu 13 da laifin fashi da makami

Yace: "Jami'in sojan yana amfani da kayan sarkinshi wajen tafiyar da motocin da yan fashin suka sato da kuma sayarwa.

Gugun yan fashi wadanda hukumar SARS suka kasance suna nema ruwa a jallo sune wadanda suka addabi matafiya a titin Ogbomoso-Ilorin, jihar Legas, Kwara da wasu jihohi a kasar Yarbawa."

KU KARANTA: Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Ramalan Yero ya gurfana gaban EFCC

Sunayen yan fashin sune: Lateef Isa, 25; Taiwo Yekini, 23; Kehinde Yekini, 23; Tunji Ismail, 23; Adeyemo Babajide 23; Saka Jamiu, 20; Akin Akingbade 35; Mudashiru Abdullahi, 29; Rasheed Adeniran, 26; Lukman Jimoh, 35; Dauda Lamidi, 24; da Waheed Ganiyu, 30.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel