Gaskiyar magana: Duk masu danganta Musulunci da ta’addanci wawaye ne – Inji Paparoma

Gaskiyar magana: Duk masu danganta Musulunci da ta’addanci wawaye ne – Inji Paparoma

Shugaban Kiristocin Duniya mabiya darikan Katolika, Paparoma Francis ya bayyana duk masu danganta addinin Musulunci da ta’addanci a matsayin wawaye, shashashai, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Paparoma ya bayyana haka ne cikin wata hira da yayi da wata jarida a kasar Italiya, a ranar da aka mayar da gawar Paparoma John na 23 zuwa garinsa dake arewacin kasar Italiya.

KU KARANTA: Yansanda sun kwato sandar ikon majalisar Dokokin jihar Gombe da yan majalisar suka sace

Gaskiyar magana: Duk masu danganta Musulunci da ta’addanci wawaye ne – Inji Paparoma
Paparoma

“Me yiwua ne kaji mutane da dama suna danganta Musulunci da ta’addanci, amma wannan maganan karya ne, kuma wawanci ne.” Inji Paparoma Francis.

Bugu da kari Paparoman ya bayyana rawar da ya kamata addinai suna takawa da ya kunshi koyar da mabiyansu zaman lafiya, al’adu da kuma bayyana halaye masu kyau.

“Babban muhimmin rawa da addinai suke takawa shi ne na habbaka al’adu tare da koyar da kyawawan halaye ga mabiya da kuma ilimi na gaskiya da zai sauya dabi’un mabiya addinai.” Ini shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel