Kaico: Jaririya tamutu bayan shan nonon uwar da maciji ya sara a Indiya

Kaico: Jaririya tamutu bayan shan nonon uwar da maciji ya sara a Indiya

- Indiyawa suna mutuwa sosai daga sarin macizai

- Yawan macizan ya kai har bauta musu ake don su sarara wa mutane da cizo

- Matar ta baiwa diyar ta nono ne cikin bacci, duk sun rasu

Kaico: Jariri ya mutu bayan shan nonon uwar da maciji ya sara a Indiya
Kaico: Jariri ya mutu bayan shan nonon uwar da maciji ya sara a Indiya

Wata mata 'yar kasar India wacce maciji ya sara a baccinta kuma ta shayar da diyarta a rashin sani sun rasa rayukansu ita da 'yar ta. Inji yan sanda a ranar juma'a.

Matar mai shekaru 35 a duniya,'yar asalin jihar Uttar Pradesh bata san ma macijin ya sareta ta ba har ta tashi daga barci ta shayar da diyarta.

Yarinyar ' yar shekaru uku da uwar sun fara ciwo a ranar Alhamis. Amma ko kafin a isa asibiti, sun rasa rayukansu. Sifeton 'yan sanda Vijay Singh ya fada wa AFP

Iyalan sunga macijin a wani daki, amma ya gudu kafin a kamashi.

Za a binciki gawarwakin.

DUBA WANNAN: Shugaban kasarmu makaryaci ne - Wasu Amurkawa

India dai ta kasance gidan macizai kala 300 kuma 60 daga cikin su suna da dafi sosai, sun hada da Indian Cobra, watau kububuwa, krait, Russell' viper da kuma Saw Scaled Viper, watau sari kutub.

India tana da tarihin mace mace 46,000 a cikin 100,000 wanda sarar macizai ke kawosu a duk shekara kamar yanda American Society Of Tropical Medicine and Hygiene ta fada a 2011.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel