An dakatar da 'yan majalisar da suka sace sandar girma ta Gombe

An dakatar da 'yan majalisar da suka sace sandar girma ta Gombe

- Saura shekara 1 Dankwambo ya gama mulki wa'adi na biyu

- An sauke mataimakin majalisar a wata cuwa-cuwa a makon nan

- Yanzu kam oda ta dawo, sai dai babu sandar har yau

An dakatar da 'yan majalisar da suka sace sandar girma ta Gombe
An dakatar da 'yan majalisar da suka sace sandar girma ta Gombe

Majalisar dokoki ta jihar Gombe ta dakatar da mutane hudu na jam'iyyar APC a jiya, sakamakon guduwa da sandar majalisar a gaban idon kowa.

Shugaban masu rinjaye kuma shugaban kwamitin watsa labarai na majalisar, Mista Fabulous Amos ya fadi hakan yayin da ya zanta da manema labarai bayan taron gaggawa da majalisar ta kira.

Yace, 'yan majalisar karkashin jam'iyyar APC, Abdullahi Abubakar Maiwanka (Akko- ta yamma), Walid Mohammed (kwami - ta yamma), Mohammed A. Bello (Gombe ta kudu) da Abubakar Sadiq Ibrahim (Yamaltu ta yamma) wadanda suka yi ruwa da tsaki cikin sace sandar majalisar, an dakatar dasu daga zama hudu na majalisar.

Ya bayyana rashin jindadin shi ga abinda 'yan majalisar sukayi, inda yayi zargin sun kawo matsalar jam'iyyar su cikin tasu majalisar.

A jiya ne majiyar mu ta ruwaito cewa, Abdullahi Maiwanka ya dau sandar majalisar ya fita da ita daga zauren majalisar.

Ance Maiwanka ya je har gaban teburin majalisar lokacin da ake zaman majalisa, ya dauke sandar, ya ranta a na kare zuwa motar shi.

DUBA WANNAN: Shugaban kasarmu makaryaci ne - Wasu Amurkawa

'Yan majalisar da suka bukaci a boye sunan su sunce, ya samu taimakon Mohammed A. Bello, wanda ya riqe sajan dake tsaron majalisar har aka fice da sandar.

Kamar yanda masu shaida suka fada, 'yan sanda masu tsaron majalisar sun harbi tayoyin motar shi don tsayar dashi amma ya gudu da fasassun gilasai da satattun tayoyi.

Daga baya ya yadda motar a New Mile 3, akan hanyar Gombe zuwa Yola.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng