Abinda yasa muka matsar da taron gangamin kasa zuwa 23 ga watan Yuni - APC

Abinda yasa muka matsar da taron gangamin kasa zuwa 23 ga watan Yuni - APC

- Jam'iyyar APC ta fadi dalilin ta yasa ta sake dage ranar taron gangaminta na kasa

- Jam'iyyar ta ce an dage taron ne saboda a bawa musulmi damar gudanar da azumin watan Ramadan

- Bayan anyi taron a ranar 23 ga watan Yuni, za'a rantsar da sabbin shugabani a ranar 25 ga watan na Yuni

Jam'iyyar APC mai mulkin kasa ta yi bayyanin dalilin da ya sa ta canja ranar da za'a gudanar da taron gangamin kasa na shekara-shekara da aka saba yi daga ranar 2 ga watan Yuni zuwa 23 ga watan.

A baya, jam'iyyar ta tsayar da ranar 2 ga watan Yuni a matsayin ranar taron kamar yadda ta bayyana a sakon da ta aike wa hukumar zabe na kasa INEC sai dai mambobin jam'iyyar da yawa sun ce an matsar da ranar taron ne saboda azumin watan Ramadan da za'a kammala kafin 23 ga watan Yuni.

Abinda yasa muka matsar da taron gangamin kasa zuwa 23 ga watan Yuni - APC
Abinda yasa muka matsar da taron gangamin kasa zuwa 23 ga watan Yuni - APC

KU KARANTA: Rikcin jihar Ribas: Shugaba Buhari ya sake ganawa da gwamna Okorocha

Jam'iyyar ta cinma wannan matsayar ne bayan kwamitin shirya taron karkashin jagorancin gwamna jihar jigawa, Mohammed Abubakar Badaru ta amince da bukatar hakan.

Gwamna Badaru ya bayyana sabuwar ranar taron ne a yayinda ake kaddamar da kananan kwamitocin shirya taron a ranar Laraba kana jam'iyyar ta sake tabbatar da canjin a wata sanarwa da ta fitar a daren Alhamis.

A sanarwan da ke dauke da sa hannun sakataren yadda labarai na jam'iyyar, Bolaji Abdullahi, ya kara da cewa za'a kaddamar da sabbin shugabanin jam'iiyar a ranar 25 ga watan Yuni.

Sakansa: "Jam'iyyar APC za ta gudanar ta taron gangaminta na kasa a ranar Asabar 23 ga watan Yuni kana za'a rantsar da sabbin shuwagabanin jami'iyyar a ranar 25 ga watan Yuni."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164