Yadda kwatsam na sadu da diya ta - Mahaifiyar 'Dalibar Dapchi ta Karshe dake hannun 'Yan Boko Haram

Yadda kwatsam na sadu da diya ta - Mahaifiyar 'Dalibar Dapchi ta Karshe dake hannun 'Yan Boko Haram

Misis Rebecca Sharibu, mahaifiyar ɗalibar Dapchi ta karshe dake hannun 'yan ta'adda na Boko Haram ta bayyana yadda kwatsam ta yi gamo da ɗiyar ta, Leah, bayan watanni hudu na zaman zulumi da takaici.

Mahaifiyar dai ta bayyana cewa, kwatsam cikin duhun dare sai Leah ta bayyana sanye da tufafi masu launin ja, inda ta rungume cikin murmushi da annashuwa a fuskarta tare da furta kalamai na cewa, 'Mama na kubuta a yanzu na samu 'yanci'.

Rebecca take cewa, cikin kankanin lokaci wannan farin ciki gami da jin dadi na ta ya yanke, yayin da ta farka daga baccin da ta ke yi ashe duk wancan labari iyakar sa mafarki.

A yayin zayyana yadda mafarkin na ta ya kasance, mahaifiyar Leah ta bayyana cewa sun rungume juna tamkar ba bu abinda ka iya raba su kafin ta fara labarta ma ta irin hali da ta shiga da duk abinda ya faru a gare ta.

Yadda na sadu da diya ta - Mahaifiyar 'Dalibar Dapchi ta Karshe dake hannun 'Yan Boko Haram
Yadda na sadu da diya ta - Mahaifiyar 'Dalibar Dapchi ta Karshe dake hannun 'Yan Boko Haram

Mahaifiyar ta ci gaba zayyana labarin Leah da cewa, "Tabbas Mama na azabtu a hannun su. Mun kasance mu na kwana kan ganyayyaki inda wani sa'ilin sai na shafe tsawon kwanaki ba tare da jiki na ya ga ruwa ba amma ko kadan ba su tauye ma ni hakki wajen cima."

Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito wannan rahoto, Mahaifiyar Leah ta yi kokarin komawa baccin ta domin ci gaba da ganawa da diyar ta amma hakan bai yiwu ba.

KARANTA KUMA: Dalilin da yasa Mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi yayi murabus

Legit.ng ta fahimci cewa, wannan shine yake nuna irin damuwa da halin da Misis Rebecca take ciki a halin yanzu na rashin ganin diyar ta, inda a kullum ba ta da wata addu'a da ya wuce saduwa da diyar ta daya da ta haifa a duniya.

Leah tana daya daga cikin daliban makarantar Dapchi da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su a ranar 19 ga watan Fabrairun da ya gabata, inda suka sako sauran kuma su ka ci gaba da rike ta sakamakon rashin karbar addinin Islama da ta yi kasancewar ta mai riko da addinin Kirista.

Mahaifiyar ta kara da cewa, labarin diyar ta dai kawowa yanzu shiru kake ji tamkar shuka ta ci shirwa a sakamakon yadda gwamnatin jiha da ta tarayya suke nuna halin ko oho ga lamarin, inda ta ce cikin daliban wata daya tilo ce mai sunan A'isha ta ziyarce ta domin jajinta ma ta akan halin da ta ke ciki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng