Hotuna: Diyar sarkin Kano ta kammala karatun digiri a kasar Faransa
Diyar mai martaba sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, Khadija Yusra Sanusi, ta kammala karatun digirinta na farko a kasar Faransa, nahiyar Turai.
Khadija Yusra Sanusi ta kammala karatunta ne a sashen ilimin aikin jarida da rubutu a jami''ar Amurka da ke Clubs, Faransa.
Ba a bar mai martaba a baya ba yayinda ya samu daman halartan taron bikin yaye daliban jami'ar a birnin Faris.
Takardan shahadan Khadija yace: " Wannan takardan shahadan na nuna cewa Sanusi Khadija ta halarci jami'ar Amukra da ke Faris daga watan Satumba, 2015 zuwa Mayu 2018. An bata kwalin kammala karatun aikin jarida a ranan 24 ga watan Mayu 2018."
Khadija na daga cikin yayan sarkin Kano da suka kammala karatunsu a kasashen waje.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng