Trump barawo ne, makaryaci, mayaudari - inji Amurkawa

Trump barawo ne, makaryaci, mayaudari - inji Amurkawa

Dubban al'ummar kasar Amurka ne suka yi cincirindo a gaban wani babban Otel dake birnin New York don gudanar da zanga-zangar adawa ga Shugaban Kasar ta Amurka Donald Trump a lokacin daya halarci wani taro a mahaifarsa wadda cibiyar 'yan jam'iyyar Democrat suka hada

Trump barawo ne, makaryaci, mayaudari - inji Amurkawa
Trump barawo ne, makaryaci, mayaudari - inji Amurkawa

Dubban al'ummar kasar Amurka ne suka yi cincirindo a gaban wani babban Otel dake birnin New York don gudanar da zanga-zangar adawa ga Shugaban Kasar ta Amurka Donald Trump a lokacin daya halarci wani taro a mahaifarsa wadda cibiyar 'yan jam'iyyar Democrat suka hada.

Masu zanga-zangar sun nuna adawar su a fili ga Shugaban kasar a dai - dai lokacin da yake halartar taron, don samar da tallafin kudi a otel din New York Palace.

DUBA WANNAN: Wata ma'aikata a Najeriya ta tilastawa ma'aikatan ta biyan kudin ID Card

Al'ummar sun dinga fadin munanan maganganu ga shugaba Trump din, inda suka dinga cewa, ba sa kaunar Shugaban kasa mai rubuta shirme a shafin sa na yanar gizo wato Twitter.

Masu zanga - zangar sun rufe hanyoyi da tituna da dama a birnin na New York inda jama'ar suka dinga kiran shugaba Trump din da sunan Barawo, Makaryaci kuma Mayaudari.

A karshe dai sai da jami'an tsaro suka jibge manyan - manyan motoci a gaban ginin otel din sannan suka tarwatsa masu zanga-zangar da karfin tsiya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel