Yanzu-Yanzu: Kotu ta bayar da belin Sanata Jonah Jang
Babban kotun da ke garin Filato ta bayar da belin tsohon gwaman jihar Sanata Jonah Jang.
Mai sharia'a Justice D.D Longi ne ya bayar de belin Sanata Jang tare da Yakubu Pam wadanda ake tuhuma da laifukan masu alaka da rashawa.
Kotun ta amince da bayar da belin ne a kan wadandan ka'idojin ...
1) Sanata sai kawo mutane biyu da zasu tsaya masa kuma daya daga cikinsu ya kasance basareken gargajiya mai sanda daraja ta daya kana sai sun bayar da jinginar N100 miliyan kuma su kasance mazauna garin Jos.
2) Sanatan zai bawa kotu Fasfo dinsa ta tafiya kasashen waje
Shi kuma Pam, ka'idan belinsa shine
1) Ya gabatar da mutane biyu da zasu tsaya masa kuma daya daga cikin su ya kasance ma'aikacin gwamnati ne mai mukamin Permanant Sakatare ko makamancin haka kuma kowanensu zai bayar da jinginar N50 milyan.
A halin yanzu, magoya bayan tsohon gwamnan sun mamaye titunan garin Jos inda suke ta murnar bayar da belinsa da kotu tayi.
Magoya bayan suna dauke da Fostocin Sanatan tare kuma da tutar jam'iyyarsa wato jam'iyyar adawa ta PDP.
Sanata Jang dai shine ke wakiltan yankin Filato ta arewa a majalisar dattawa kuma a kwanakin nan Sanatan ya biya dukkan bashin kudin lantarki da ake bin gidan yarin bayan an kulle shi a ranar 16 ga watan Mayu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng