Jerin mutanen da zasu gwabza da Tambuwal takarar kujerar gwamnan Sokoto

Jerin mutanen da zasu gwabza da Tambuwal takarar kujerar gwamnan Sokoto

- Tsohon Ministan Al'adu da yawon shakatawa, Sanata Bello Jibril Gada, ya bayyana kudurin sa na neman takarar gwamnan jihar Sokoto a karkashin inuwar jam'iyyar APC a zabe mai gabatowa na shekarar 2019

- Har Ila yau, tsohon kwamishinan kudi da kananan hukumomi, Alhaji Faruk Yabo, shima ya bayyana kudurin sa na neman kujerar a APC din

Jerin mutanen da zasu gwabza da Tambuwal takarar kujerar gwamnan Sokoto
Jerin mutanen da zasu gwabza da Tambuwal takarar kujerar gwamnan Sokoto

Tsohon Ministan Al'adu da yawon shakatawa, Sanata Bello Jibril Gada, ya bayyana kudurin sa na neman takarar gwamnan jihar Sokoto a karkashin inuwar jam'iyyar APC a zabe mai gabatowa na shekarar 2019. Har Ila yau, tsohon kwamishinan kudi da kananan hukumomi, Alhaji Faruk Yabo, shima ya bayyana kudurin sa na neman kujerar a APC din.

DUBA WANNAN: Adadin mutanen da suka mutu a Najeriya cikin wata 6 sanadiyyar hadarin mota

Mutane biyun sun nuna kudurin nasu ne, duk kuwa da cewar wannan shine karo na farko na mulkin gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal a jam'iyyar ta APC. To sai dai kuma akwai kishin-kishin cewar Tambuwal din zai iya fitowa takarar shugaban kasa a wata jam'iyyar daban, hakan shine ya bawa mutanen damar bayyana manufofin su na son takarar.

Da yake jawabi ga magoya bayan sa a gidan sa dake Sokoto a karshen wannan satin, Sanata Gada yace shekaru uku ya isa mutanen jihar su gane cewar gwamnatin Tambuwal ba abinda tayi musu. A cewar sa jihar ta fuskanci matsaloli da yawa, ciki har da matsalar ruwan sha a wasu yankunan.

Ya bayyana abubuwa hudu, wanda yace zai kawo wa al'ummar jihar domin ganin cigaba ya wanzu a fadin jihar.

Abubuwa hudun sun hada da: Bunkasa noma, gyara kananan hukumomi, bunkasa harkar ilimi da kuma kawo cigaba ga matasa akan harkar wasanni.

Yace da irin kyautar lambar yabo ta kasa da kuma sarautar da aka bashi ta Sarkin Noman Sarkin Musulmi, yana da tabbacin cewar zai kawo canji sosai a harkar noma a jihar.

Hakazalika shima, Faruk Yabo wanda ya shiga tseren, ya nada tsohon manajan gidan talabijin na Rima, Wafee Suka a matsayin Darakta Janar na kafar sadarwa.

Yabo ya kasance na hannun damar tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakarda Wamakko, kuma ya nemi fitowa takara a shekarar 2015, kafin a roke shi akan ya barwa Tambuwal ya fara yi kafin nan sai ya nema.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel