Cima zaune: An shirya fim din Hausa a game da kalaman Buhari a kan matasan Najeriya
A watan Afrilu ne shugaba Buhari ya yi wani furuci a kan matasan Najeriya dake nuna cewar mafi yawan su ‘yan tamore ne da basa son yin kowanne aiki. Kalaman na Buhari sun jawo barkewar cece-kuce a Najeriya.
Sai gashi yanzu haka wani furodusa a masana’antar shirya fina-finan Hausa (Kannywood), Hamza Lawal Abubakar, da ka fi sani da Dogo Dandago, ya shirya wani fim mai suna “cima zaune”, sunan day a samo asali daga kalaman shugaba Buhari.
Saidai furodusa Dogo Dandago y ace ya shirya fim din ne domin fadakar da jama’a gaskiya da muhimmancin kalaman shugaba Buhari.
Kazalika ragowar masu ruwa da tsaki a tsara shirin fim din “cima zaune”, sun bayyan cewar sun yi hakan ne bisa la’akari da yadda kalaman na shugaba Buhari suka ja hankula a ciki da wajen kasar nan, tare da haifar da cece-kuce.
DUBA WANNAN: Mas'aloli 6 da suka dade suna ciwa masu azumi tuwo a kwarya
Abba Almustapha da aka fi sani da Abba Ruda ne ya fito a matsayin tauraron shirin fim din inda aka nuna shi a matsayin wani matashi day a shafe shekaru biyar yana neman aiki da kwalin san a digiri a fannin injiniya amma aikin ya gaza samuwa, hakan ta saka shi fadawa cikin abokai cima zaune.
Ya zuwa yanzu ba a bayyana ranar da Fim din zai fito kasuwa ba. Bayan Abbab Ruda akwai fitattaun jarumaia a cikin shirin da suka hada da Sulaiman Bosho.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng