Gwamna Ganduje ya Musuluntar da Maza 21, Mata 40 daga cikin maguzawan jihar Kano (Hotuna)
- Gwamnan jihar Kano ya musuluntar da Maguzawa a fadar gwamnatin jihar Kano
- Maguwazan sun hada da Mata 40, Maza 21, kuma sun fito ne daga Sumaila
Eh, dama Hausawa na cewa suna linzami ne, ya kan bi mai dauke da shi, kwatankwacin haka ne ya faru da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje wanda ake yi ma lakabi da Khadimul Islama, watau mai yi ma addinin Musulunci hidima.
KU KARANTA: Hankaka maida Dan wani naka: Wani Gwamna ya zama Uba ga wani zakakurin Yaro
Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba 23 ga watan Mayu, ranar Azumi na 7, gwamnan jihar ya ci sunansa mai yi ma Musulunci hidima, inda ya baiwa wasu maguzawa su sittin da daya, 61, Kalmar shahada a masallacin fadar gwamnatin Kano.
Maguzawan da suka karbi Musulunci a hannun gwamna Ganduje sun hada da mata guda arba’in, 40, da kuma Maza ashirin da daya, 21, kuma dukkansu daga karamar hukumar Sumaila, kuma dukkaninsu sun halarci zaman karbar shahadar.
Sai dai wannan dace da maguzawan nan suka yi sun same shi ne a karkashin gidauniyar Ganduje, inda gwamnan ta gidauniyar tasa ya yi alkawarin gina musu Makarantar Islamiyyu don su koyi addinin Musulunci cikin sauki, sa’annan ya bi su da kudi naira dubu ashirin ashirin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng