Kamfanin Google zai kashe miliyan 700 a Najeriya kan kamfunna masu neman jari

Kamfanin Google zai kashe miliyan 700 a Najeriya kan kamfunna masu neman jari

- A ranar laraba ne Google ta gabatar da Google Impact Challenge Nigeria 2018 don habako da 'yan kasa domin samun amfanin ta

- Manajan tallata Google na kasa, Affiong Osuchukwu, a gurin Bude taron a jihar Legas yace, Google zata saka dala miliyan biyu a manyan aiyuka fasaha don cimma manufofin su

Kamfanin Google zai kashe miliyan 700 a Najeriya kan kamfunna masu neman jari
Kamfanin Google zai kashe miliyan 700 a Najeriya kan kamfunna masu neman jari

Kungiyar dillancin labarai ta Najeriya ta ruwaito cewa kudin dai ba sai an kara musu riba ba gurin biya an sadaukar dashi ne gurin cigaban walwala.

"Wannan ne Karo na farko da muka yi GIC a Afirika. Da yawan aiyukan da mukayi da ba a Afirka ba suna tafiya lafiya lau kuma muna da niyyar haskaka su tare da basu tallafi na kudi domin kirkire kirkire."

"Mun yarda fasaha zatayi taimako a kungiyoyin gida da waje don su cimma manufofin su da kuma magance wasu daga cikin matsalolin da suke takurawa Nahiyar."

"Mun kosa mu waiwayi mutane da ke amfani da fasaha ta sababbin hanyoyin kawo cigaba ga al'ummar su."

"Muna kuma so mu kara bayani akan halin nagartar da walwala take a Najeriya a yau, kuma mu karfafa kamfanonin da basu bukatar riba da suyi amfani da fasaha don cimma manufofin su." Osuchukwu tace.

DUBA WANNAN: Wani gardi yaki barin gida a Amurka har iyayen sun kai qararsa

Ta shawarci kamfanoni marasa neman riba na najeriya dasu mika bukatar su don samu daga cikin dala miliyan biyu. Tace za a bude kofar karbar tallafin har zuwa nan da wata shida.

Osuchukwu tace wata kungiyar alkalai ce zata tantance wadanda suka dace da kuma zabe da za a ba mutane damar yi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng