Hankaka maida Dan wani naka: Wani Gwamna ya zama Uba ga wani zakakurin Yaro

Hankaka maida Dan wani naka: Wani Gwamna ya zama Uba ga wani zakakurin Yaro

Gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode ya sanar da daukan wani zakakurin yaro a matsayin dansa, inda yayi alkawarin daukar nauyinsa har Illa Masha Allahu.

Gwamna Ambode ya bayyana haka ne a yayin da ake gudanar da bikin yaye daliban jami'ar jihar Legas, LASU na shekarar 2016/2017.

KU KARANTA: Tashin hankali ba’a sa miki rana: Wata Giwa ta mitsitstsike wani manomi har lahira a gonarsa

Wannan yaro ba wani bane Illa wani zakakurin dalibin jami'ar Legas, Ogunsanya Fuad wanda ya kammala digirinsa da sakamako mafi daraja a kafatanin jami'ar.

Hankaka maida Dan wani naka: Wani Gwamna ya zama Uba ga wani zakakurin Yaro
Dalibi Fuad

Bugu da kari gwamnan ya baiwa Fuad kyautar kudi naira miliyan biyar, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Hakazalika Gwamna Ambode ya yi alkawarin daukar nauyin yaron ya cigaba da karatunsa a duk kasar da yake sha'awar zuwa yayi karatu.

Daga karshe Gwamnan ya bayyana cewa Allah ne ya ciyar da wannan yaro da zuwansa wannan taro, saboda dama rabon kwado baya hawa sama.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel