Wani Matashin Malami ya yi lalata da 'Dalibar sa 'Yar shekara 4 a jihar Neja

Wani Matashin Malami ya yi lalata da 'Dalibar sa 'Yar shekara 4 a jihar Neja

Mun samu rahoton cewa, a ranar Talatar da ta gabata ne wani matashin malamin makaranta mai shekaru 19 a duniya, Victor Opute, ya yi lalata da wata dalibar sa mai shekaru 4 a birnin Minna na jihar Neja.

Majiyar rahoton ta bayyana cewa, wannan lamari ya bayyana ne yayin da dalibar da nuna wannan matashin malamin da manuniyar yatsan ta da cewar shi ya yi ma ta wannan aika-aika.

Kamar yadda jaridar ta The Nation ta bayyana, daya daga malaman makarantar ne ya jiyo koken ta, inda ya riske ta kwatsam cikin wani bandaki na makarantar da wannan lalataccen bawa ya aikata ta'asa kuma ya kama gaban sa.

Wani Matashin Malami ya yi lalata da 'Dalibar sa 'Yar shekara 4 a jihar Neja
Wani Matashin Malami ya yi lalata da 'Dalibar sa 'Yar shekara 4 a jihar Neja

A sanadiyar haka aka tsananta bincike cikin malamai maza 19 da makarantar da kunsa, inda wannan daliba ta yi nuni izuwa Victor kuma nan take ya amsa laifin sa ba tare da wata gardama ko jayayya ba.

KARANTA KUMA: Da ni ne kai da ban nemi Shugabancin Najeriya ba yayin da na haura shekaru 70 - Kanal Hameed ga Shugaba Buhari

Legit.ng ta fahimci cewa, hukumar tsaro ta NSCDC da aka gayyato domin gudanar da wannan bincike da ya gaba da wannan matashin malami, inda ta danka shi a hannun hukumar kare hakkin kananan yara domin gurfanar da shi.

A yayin haka kuma, Shugaban hukumar na reshen jihar, Mista Philip Ayuba, ya tabbatar da afkuwar lamari, inda ya bayyana cewa, jami'an hukumar za su ci gaba da bibiya ta diddigi akan lamarin domin tabbatar da an hukunta Malamin makarantar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel