Tramadol da Kodin: Majalisa tayi doka don hukunta masu safarar haramtatun magungunan
A jiya Talata ne majalisar wakilai ta gabatar da wata kudiri na sanya tarar N2 miliyan da kuma zaman gidan kurkuku na shekaru biyu a kan kamfanoni aka kama suna safarar magungunan da aka haramta masu dauke da Kodin ko kuma Tramadol.
Wadanda kuma ba a karkashin wata kamfani suka aikata laifin ba, majalisar ta bukaci a ci su tarar N500,000 ko zaman gidan yari ne shekaru biyu ko kuma a hada wa mai laifin dukkan hukuncin biyu.
Kudirin kuma ta ce idan kamfani ne aka samu da karya dokar, dukkan direktoci, manajoji, abokan hulda da yan kwamitin amintatun kamfanin za su fuskanci hukuncin kamar sune suka aikata laifin da kansu.
KU KARANTA: Lalaci: Wani magidanci ya yi wa matarsa duka saboda ta gaza ciyar dashi
Kudirin ta Betty Apaifi daga jihar Rivers (PDP) ta gabatar za tayi kwaskwarima ne a kan dokar Abinci, magunguna da ababe masu kama da su Act Cap. F33 na dokar kasar Najeriya 2004.
Wadda ke jagorantar muhuwarar, Mrs. Apaifi ta ce "A kasar nan tsakanin watan Janairu - Disambar 2015, an samu marasa lafiya 1,044 da aka yiwa magani a asibitoci 11 a kasar nan a karkashin wani shirri na sanya ido kan yaduwar cututuka (NENDU)."
Ta kara da cewa, tun shekarar 2015, kodin ya kusa dara tramadol a matsayin kwayar da mutane sukafi shan ta ba bisa ka'ida.
Ta cigaba da cewa yan majalisar za su bayar da gudunmawarsu wajen yaki da ta'amulli da miyagun kwayoyi da abinci wanda hukumar NAFDAC bata amince dasu ba.
Majalisar ta amince da kudirin bayan kakakin majalisar, Yakubu Dogara ya gabatar da kudirin don yin mahawara. An kuma mika kudirin ga kwamitin lafiya don daukan matakan da suka dace.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng